Ma’aikatar harkokin kula da aikin ƴan sanda a Najeriya sun kori wasu jami’ai biyu da su ke aiki dakataccen ɗan’sandan da ake zargi da hannu wajen shigo da miyagun ƙwayoyi.
Ma’aikatar ta kori Sunday Ubua mai muƙamin mataimakin kwamishinan yan sanda da kuma James  Bawa mai mukamin mataimakin sufritandan ƴan sanda.

Korar jami’an ta biyo bayan hannu da aka samesu wajen taimakawa dakataccen jami’in ɗan sanda Abba Kyari wajne hada-hadar miyagun ƙwayoyi.

Zartar da hukuncin da hukunmar ta yi wanda su ka aikewa sufeton ƴan sandan Najeriya Usman Alƙali Baba a ranar Laraba.

Hukumar ta yi zargin jami’an da taimaka wa wajen sabon faifan bidiyon da aka hango muƙaddashin kwamishinan ƴan sanda Abba Kyari na bayar da hasafi domin shigar da hodar iblis.

Haka kuma hukumar ta mika ƙorafin zuwa ga hukumar  hana sha da fataucin miyagun ƙwayoyi  a Najeriya NDLEA domin faɗaɗa bincike tare da ɗaukar mataki na gaba  a kan waɗanda ake zargi.

Tuni jami’an ƴan sanda su ka kama Abba Kyari bayan hukumar NDLEA ta bayyana ƙarara ta na nemansa ruwa jallo.

Leave a Reply

%d bloggers like this: