Daga Amina Tahir Muhammad

Wani mutum mai shekaru 76 a duniya Samuel Akande a yau Alhamis ya maka matarsa mai suna Gift a gaban wata kotu ta Iyana-Ipaja, bisa zargin ƙin yi wa ƴarsa abinci a lokacin da ta ziyarce su.

Akande, wanda ke zaune a Idimu a jihar Legas, ya shaida wa kotu cewa ya yi aure da Gift, mai shekaru 37 a duniya shekaru goma sha uku da suka gabata.

Ya kuma zargi matarsa ​​da bin zama, sannan ta hana shi yin jima’i da ita.

“matata ba ta saurare na. ba ta zama a gida sannan kuma ta na yawan faɗa da masu gidan haya.

“Wani mutum ya zo gidana tare da wani wanda ya shaida min cewa yana kwana da matata.

“Matata ta kawar da wannan zargi lokacin da na fuskance ta a cewarsa.

Sai dai matar da ake tuhuma a bisa laifukan da ya lissafa, ta ce ba ta da masaniya a kan ziyarar da ,yar tasa za ta kai musu.

Alƙalin kotun ya P.O Adejanyu ya sulhunta ma’auratan tare da roƙon mijin ya ba ta dama da  ƙarshe a nan gaba.

Leave a Reply

%d bloggers like this: