Ma’aikatar Muhalli a Jihar Nasarawa ta kama gawayi mai tarin yawa wanda aka samar ba tare da iznin gwamnati ba.

Tun a baya gwamnatin jihar ta yi gargadin a kan sare itatuwa ba bisa ka’ida ba da kuma ƙone bishiyoyi na nufin samar da gawayi.
Kwamishinan muhalli a jihar Yakubu Kwanta ne ya bayyana haka a wata hira da manema labarai bayan ya ziyarci wurin da aka tara gawayin da aka kama a garin Uke da ke karamar hukumar Karu a jiya Juma’a.

Ya ce gwamnatin jihar ta haramta samar da gawayi a jihar tun a shekarar da ta gabata da nufin daƙile matsalolin da hakan ke haifarwa.

Kwanta ya bayyana wadanda ke karya umarnin gwamnatin jihar a matsayin marasa kishin kasa wadanda suka dukufa wajen lalata dazuzzuka ba tare da la’akari da illolin da hakan ka iya haifar wa sauyin yanayi ba.
Kwamishinan ya ce sare itace a jihar babbar barazana ce ga al’amuran da su ka shafi sauyin yanayi a jihar.
Sannan ya jaddada cewar gwamnatin jihar ba za ta lamunci ci gaba da sare bishiyu a dazukan jihar da nufin samar da gawayi kuma duk wanda aka kama zai fuskanci hukunci mai tsananin gaske.