Wasu ‘yan bindiga sun kai farmaki kauyen ‘Yar Tsakuwa da ke karamar hukumar Rabah a jihar Sakkwato, inda suka yi awon gaba da mutane tara, ciki har da kansilan yankin, Lawali Bello LBY

Mata biyu da ƴar tsohon Kansilan yankin, Alhaji Abdullahi Garba na daga cikin wadanda aka yi garkuwa da su.

Wani daga cikin mazauna yankin ya ce ‘Yan bindigar sun zo ne da tsakar daren juma a wayewar Asabar kuma su ka yi ta ƙaddamar da hare-haren har zuwa karfe 2:50 na dare.

Rahotanni sun nuna cewar maharani sun yi ta balle gidaje da shaguna da suka hada da shagunan sayar da magunguna, inda suka yi awon gaba da kayayyaki da dama.

A cewar wani mai suna Abdullahi, barayin sun sace babura da kayan abinci da magunguna iri-iri a garin.

Ya ce sun yi garkuwa da mutane sama da 20 amma sun saki wasu yayin da suka nufi cikin daji da su.

Ya ce a halin da ake ciki mutane tara su na tare da su, ciki har da Kansilanmu mai ci da matansa da ƴaƴansa.

Rundunar yan sandan jihar ba ta ce komai a dangane da harin da aka kai ba.

Leave a Reply

%d bloggers like this: