Ƙungiyar ɗalibai a Najeriya NANS ta umarci mambobinta da ke jihohi 36 da babban binrin tarayya Abuja da su toshe dukkanin manyan hanyoyin zirga-zirga mallakin gwamnatin tarayya.
Shugaban ƙungiyar na ƙasa Asefon Sunday ne ya sanar da haka a wata sanarwa da su ka sanya wa hannu shi da sakataren ƙungiyar.
Matakin ƙumgiyar na ƙasa ya biyo bayan yajin aikin da ƙungiyar malaman jami’a a Najeriya ASUU su ka tsunduma na wata guda bisa rashin cika musu alƙawuran da gwamnati ta yi musu tsawon lokaci.
Ƙungiyar ɗaliban ta ce matakin rufe manyan hanyoyin ya zo ne bayan matsayar da ƙungiyar ta cimma a yayin zaman da ta gudanar a jami’ar Sokoto.
Ƙungiyar ta ce yajin aikin malaman jami’an na mayar da ɗaliban baya tare da ja musu asara wajen biyan kuɗaɗen haya da sauran abubuwan da ɗaliban ke zamto musu asara a sanadiyyar yajin aikin.
Sanan ƙungiyar ta ce a ranar Litinin 28 ga watan da mu ke cki za ta yi gangami domin jan hankalin gwamnati na kawo ƙarshen yajin aikin baki ɗaya.
Ƙungiyar malaman jami’a a Najeriya ta tafi yajin aikin wata guda domin nuna fushinsu a kan martaba bukatun da su ka miƙa wa gwamnatin tarayya.