Daga Khadija Ahmad Tahir
Kakakin ‘yan sandan jihar Kaduna ASP Muhammad Jalige shi ne ya bayyana cewa rundunar ta samu nasarar dakile harin a lokacin da ‘yan bindigan su ka yi nufin kai wa babbar hanyar Kaduna zuwa Abuja hari.
Kakakin ‘yan sanda ya kara da cewa ‘yan sandan sun kai daukin ne a lokacin da su ka samu rahoto a kan harin inda su ka gano cewa ‘yan bindigan masu tarin yawa su na cikin kauyen Kurmin kare da ke karamar hukumar Chikum wanda ya ke kan hanyar Jihar Kaduna zuwa Abuja.
Kakakin ya ce ‘yan bindigan sun zo ne domin kai munanan hare-hare wasu gurare inda ba a san ko ina za su kai ba.
A yayin dakile harin ‘yan sandan sai da su ka yi musayar wuta da ‘yan bindigan daga bisani su ka fatattake su.
Muhammad Jalige ya tabbatar da kwato bindiga kirar AK 47 da harsasai masu tarin yawa.
Sannan jami’an na ‘yan sanda su ka bayyana cewa wasu daga cikin ‘yan bindigan sun jikkata.
Muhammad Jalige ya kara da cewa rundunar ‘yan sandan Jihar za ta cigaba da binciko bata garin a duk inda su ke domin magance su
Sannan ya yi kira ga mutanem da ke kauyukan da su ke kusa da yankin da aka fatattaki ‘yan bindigan da zarar sun ji abinda basu gamsu da shi su yi gaggawar kai rahoto ga jami’an tsaro.