Wasu ƴan bindiga sun kai hari Galadiman Kogo a jihar Neja sannan su ka ƙone gidaje masu tarin yawa.

Lamarin na zuwa ne a daren Lahadi wayewar Litinin daidai lokacin da mayaƙan Boko Haram su ka kai hari jihar Borno tare da harba rokoki a Gamboroun-Ngala.

Mutane a Galdiman Kogo ta jihar Neja sun tsere daga gidajensu yayin da su ka samu labarin ƴan bindiga na shirin kai hari garin.

Bayan fitar da wasu da dama na garin su ka yi yan bindigan su ka kai harin tare da kone gidaje da dama sannan sun shafe fiye da awanni biyar a cikin garin.

wani mazaunin garin ya tabbatar da cewar yan bindigan sun ƙone foye da rabin gidajen garin ƙurmus.

Mutanen garin sun nemi mafana a wani sansani dake ƙaramar hukumar Shiroro ta jihar Neja kafin gwamnati ta kai msuu ɗauki.

Rahotanni sun tabbatar da cewar maharan sun saka abin fashewa a wata mota wanda hakan ya yi sanadiyyar rasa rayukan mutanen da ke cikin motar.

Ana zargin mayaƙan Boko Haram da kai hare-hare a jihar Neja kamar yadda gwamnatin jihar a baya ta bayana cewar su na kafa sansani a wasu dazukan jihar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: