Fadar shugaban ƙasa ta ce shugaban Najeriya Muhammadu Buhari zai duba tare da yin abin da ya dace a kan sabuwar dokar hukumar zaɓe da aka sake miƙa masa.

Mai magana da yawun shugaba Buhari Femi Adesina ne ya sanar da hakan a wani saƙon mayar da martani a kan wasu ƙungoyoyi da su ka fara sukar shugaban kan jan ƙafar da ake waje sanyawa dokar hannu.

Femi Adesina ya gagadi masu alaƙanta hakan da siyasa wanda ya ce akwai batu na tabarɓarewar tsaro da ƙasar ke fuskanta a halin yanzu.

Ya ce majalisar zartarwa a Najeriya za ta duba tare da yin duk mai yuwuwa wajen gudanar da abin da ya dace a kan sabuwar dokar.

Sannan ya sake nanata damar da shugaban yake da ita na kwanaki 30 kafin sanya hannu a kan sabuwar dokar kamar yadda kundin starin muli ya bashi dama.

Wasu ƴan Najeriya na kallon jan ƙafar da shugaba ke yi wajen sanya hannu a matsayin cikas da hakan zai iya haifarwa a zaɓen da ake tinkara a shekarar 2023.

Ya ce shugaban zai sanya hannu a cikin wa’adin da ya ke da shi na wata guda domin duba sabuwar dokar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: