Yan sanda a Abuja sun gurfanar da wani matashi mai suna Mamman Aminu da ake zargi da satar wata kujera a cikin wata makarantar firamare.

A na zargin matashin da shiga makarantar Pilot Science Primary School da ke Gwagwalada a Abuja
An gurfanar da matashi a gaban kotu ranar Litinin bayan jami’an sa kai sun gano ya saci wata kujera da sauran kayayyaki da kuɗinsu ya kai naira dubu sittin.

Sai dai matashin ya musanta zargin da ake masa.

Alkalin kotun ya bayar da belin matashin a kan kiɗi naira dubu ɗari da kuma mutum guda da zai tsaya masa sannan ya dage sauraron karar zuwa ranar 23 ga watan Maris mai kamawa.