Daga Amina Tahir Muhammad

Tsohon gwamnan Kano kuma tsohon sanatan Kano ta tsakiya Rabi’u Musa Kwankwaso ya ce sun kafa ƙungiyar ne domin ceto Najeriya daga halin da ta shiga.

A yau Talata ne tsohon gwamnan jihar Kano, Rabi’u Kwankwaso, ya bayyana kafa runduna ta uku, karkashin inuwar National Movement domin tinkarar siyasa a shekarar 2023.

Sauran a tawagar da ke tare da shi sun haɗa da Sanata Suleiman Hunkuyi na jihar Kaduna, tsohon ministan matasa da raya wasanni, Solomon Dalong, Buba Galadima, da sauran fitattun ‘yan Najeriya.

A cewarsu  za su karɓe mulki daga hannun jam’iyyar All Progressives Congress APC a shekarar 2023.

TNM ta ce tana sane da kwakkwaran aikinta na ceto Najeriya daga wargajewar da ta yi a yanzu.

Yayin da ta yi alkawarin ceto dimokuradiyya da ceto al’ummar kasar, TNM ta ce ta shirya fafutukar kwato ran Najeriya daga hannun APC da jam’iyyar PDP.

Da yake jawabi a wajen taron, wanda ya shirya taron tsohon gwamnan Kano Rabi’u Kwankwaso, ya ce burinsu na haɗa kai domin ceto ƙasar ne ya sa su ka ɗakko sabuwar jam’iyyar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: