Wasu ƙungiyoyi masu zaman kansu haɗin gwiwa da ƙungiyoyin kare haƙƙin ɗan’adam sun gudanar da zanga-zanga a jihar Ogun yau Alhamis.

Ƙungiyoyin sun gudanar da zanga-zangar ne domin nuna fushin su a kan yawan kashe-kashen mutane da ake yawan yi a jihar.
Ƙungiyoyin sun bayyana yawan yin garkuwa da mutane, harin ƴan bindiga, ta’ammali da miyagun ƙwayoyi waɗanda su ka ce ya na yawan ƙaruwa.

Kwamared Yinka Folarin ne ya jagoranci zanga-zangar wanda su ka zagaya cikin Abeokuta zuwa majalisar dokokin jihar sannan su ka zarce zuwa gidan gwamnatin jihar.

Shugaban majalisar dokokin jihar Olakunle Oluomo ya yi Alla-wadai da yawan kashe-kashen da ake yawan yi a jihar.
Sanna ya buƙaci jami’an tsaro da su ƙara ƙaimi wajen ganin an daƙile yawan kashe-kashen mutane da ake yawan yi a jihar.
Olakunle ya ƙara da cewa za su tabbatar sun sa ido tare da aiwatar da duk wata doka da za ta kawo ƙarshen kashe-kashe da ake yawan yi afadin jihar baki ɗaya.