Bayan sanya hannu a kan sabuwar dokar hukumar zaɓe da aka sabunta wadda shugaban Najeiya Muhammadu Buhari ya saya wa hannu a jiya Juma’a hukumar zaɓe mai zaman kanta a Najeriya INEC ta kira mambobinta taron gaggawa domin tattaunawa a kan sabuwar dokar.

Kiran gaggawar ya zo ne bayan sanya hannu, kuma za su tattauna a kan sabuwar dokar da za ta taimaka wajen cimma sabbin tsare-tsare a yayin zaɓen 2023 mai gabatowa.
Kwamishinan zaɓe na ƙasa kuma shugaban kwamitin wayar da kai a kan al;amuran zaɓe Festus Okoye ne ya sanar da haka a wata sanarwa da ya fitar.

Ya ce sabuwar dokar ta ƙunshi sabbin cigaba wanda za a aiwatar da su a yayin zaɓen shekarar 2023 da ake tunkara.

Hukumar ta amince tare da yin farin ciki a kan sabbin stare-tsaren da aka samar wanda aka tabbatar za su taimaka wajen tsaftace zaɓe a Najeriya.
Sama da shekaru 10 aka shafe kafin gudanar da gyare-gyare na dokar zaɓe a Najeriya wanda a yanzu aka tabbatar da ita a shekarar 2022 da mu ke ciki.