Wasu da ake zargi ƴan bindiga ne sun sace wasu amare yayi da su ka kai wasu tagwayen hare-hare a ranakun Asabar da Lahadi.

Ƴan bindigan sun kai hari wasu garuruwa 10 da ke ƙaramar hukumar Lavun ta jihar Neja.
Maharan sun shga garururwan a kan babura ɗauke da muggan makamai ciki har da bindigu ƙirar AK47 a tare da su.

Harin farko sun kai a daren Asabar sannan su ka sake koma wa a safiyar ranar Lahadi har su ka tafi da sabbin amaren da aka ɗaura musu aure.

Wani ɗan uwa ga amaren da aka sace ya shaida wa Daily Trust cewar ƴan bindigan sun tafi da amare ne yayin da su ka koma kai hari a washegarin Asabar da su ka kai harin farko.
Sai dai a ranar Lahadi ba su sami mutane da dama a garin ba kasancewar wasu sun tsallake sun bar gidajen su bayan ƴan bindigan sun kai harin farko.
Kwamishinan ƙananan hukumomi a jihar Emmanuel Umar ya tabbatar da kai harin tare da sace amaren.
Ya ce ƴan bindigan sun kai hari ƙaramar hukumar Lavun ne bayan da su ka kai wasu hare-hare ƙananan hukumomin Wushishi da Mashegu a jihar Neja.