Cibiyar SRZ Charitable Foundation ce ta karrama guda cikin ma’aikatan Mujallar Matashiya Amina Ɗahir Muhammad bayan lashe gasar a fagen karatun addinin musulunci.

An yi taron karramawar da wasu da su ka lashe gasa a sauran ɓangaren sai kuma wasu ɗaiɗaikun mutane.

Shugaban cibiyar SRZ Charitable Foundation Ilyas Abdulhamid (Abu Muhammad) ya ce an shafe shekaru uku cibiyar na aikin taimakon mutane masu ƙaramin ƙarfi.

Cibiyar na aikin kai tallafi gidan marayu da asibitoci da sauran unguwannin marasa ƙarfi.
A yayin taron da aka yi ranar Lahadi, mutane daban-daban ne su ka halarta ciki har da wasu daga ɓangaren sarautar gargajiya a jihar Kano.
Waɗanda aka karrama sun bayyana jin daɗinsu a bisa karramawar da aka yi musu.
Mutane daban-daban ne su ka halarci taron.