Kwamishinan yaɗa labarai Malam Muhammad Garba ne ya sanar da haka ya ce mutane huɗu an sallame su ne bayan kafa wani kwamiti don yin bincike a kansu.

A sallami Audu Baba Aliyi da Baba Audu sai kuma Abdullahi Nuhu Idris da Abdulmuminu Magami.

Bayan samun ƙorafi a kan mutanen waɗanda ake zargi da siyar da wasu filaye gwamnatin ta kafa wani kwamiti domin gudanar da bincike wanda ya gano su na da hannu a ciki.

A na zargin mutanen huɗun da siyar da filaye, bayar da takardun boge, da kuma bayanan ƙarya.

Gwamnatin Kano ta ja kunnen sauran ma’aikatan gwamnati da su mayar da hankali a kan aikin su tare da gudanar da hi kamar yadda doka ta tanada.

Leave a Reply

%d bloggers like this: