Labari ne na gaskiya da ya faru shekaru aru-aru da su ka gabata.

Masana’antar shirya fina-finan Hausa ta Kannywood ta zarce tunanin masu tanani musamman wanda yasl san yadda masana’antar ta faro sama da shekaru talatin baya zuwa yanzu.
Na yi imanin wani zai gaskata abin da nake faɗa cewar an samu cigaba ƙwarai da gaske wanda hakan ya sa duniya ta san da zaman masana’antar a matsayin masana’antar da ke bunƙasa sakamakon irin nagartattun fina-finan da ake samarwa duk kuwa da ƙalubalen kuɗi sakamakon ƙarancin samun tallafi ko zuba jari daga ɓangaren gwamnati da sauran masu ruwa da tsaki kan harkokin fim na duniya.

Zuwa yanzu masana’antar shirya fina-finan Hausa ta ɗauki wata sabuwar turba ta cigaba, wanda nan gaba kaɗan duniya za ta ƙara gamsuwa da ayyukan Kannywood Wanda hakan zai sa masana’antar fara karɓar manyan lambobin yabo a mataki na duniya sakamakon fara ɗaukar wani ingantacce kuma nagartaccen sabon shirin fim mai dogon zango mai suna “Lulu Da Andalu” wanda dukkanin abinda labarin ya ƙunsa abu ne da ya faru a zahiri.

Mansa Musa wani shahararren mai dukiya ne ɗan ƙasar Mali wanda tarihi ya tabbatar da cewa ya taɓa zama mutumin da babu wanda ya kai shi tarin dukiya a faɗin duniya, ya yi mulkinsa a matsayin Mansa na Mali tsakanin shekara ta 1312 sannan kuma ya rasu a shekara ta 1337.
Sai kuma kwatsam a wannan zamanin namu na shekara ta 2022 aka sami wani bawan Allah wanda burinsa shine ya gano inda dukiyar Mansa Musa take domin ya mallaketa, sai dai kafin gano inda dukiyar Mansa Musa take dole sai an taso da wasu hatsabiban aljanu guda biyu wato LULU da ANDALU daga wani dogon barcinsu na shekaru sama da 700 da suka gabata.
Haka kuma shirin fim ɗin zai nuna yadda dangantaka da mu’amular rayuwa ke gudana tsakanin bil’adama da Jinnu ke kasancewa ta yadda mutum da aljanu za su yi aiki tare wajen gano maɓoyar da aka killace tarin dukiyar.
Sannan bil’adama da jinnu za su yi amfani da tsafi wajen gudanar da aikinsu. Ko ta yaya hakan zai yiwu? Wannan na daga cikin tarin tambayoyin da mutane ke yi a dangane da shahararren wasan kwaikwayo da aka fara ɗauka mai suna Lulu Da Andalu.
Domin tabbatar da yiwuwar wannan aikin fim mashiryin shirin din Lulu da Andalu ya ɗauki ƙwararrun masana aikin shirya fina-finai da jarumai maza da mata domin tabbatar da ganin wannan gagarumin aiki ya zama gaskiya, sannan hakan ya gamsar da duniya makallata fina-finai a fadin duniya.
Wannan wani abin yabawa ne bisa bijiro da wannan aiki duk kuwa da yanzu haka ana kan gudanar da shi.
Shirin fim ɗin da kaso tamanin cikin ɗari sabbin abubuwa ne a cikinsa wanda ke buƙatar ƙwararru wajen aiwatar da shi, wannan ce ta sa dukkanin jaruman da ke taka rawa a cikin shirin sai da aka basu ƙwaryar-ƙwaryan horo domin ƙara sanin makamar aiki yadda ya kamata.
Daga karshe dai mu na fatan ganin Gawurtaccen shirin daga masana’antar shirya fina-finan Kannywood wanda zai gamsar da masu kallo na fadin duniya, kuma hakan zai janyo tafka muhawara a tsakanin jama’a.
Saboda haka mu jira fitowar wannan ƙayataccen shiri da zarar an kammala aikinshi.
Jinjina ga duk kanin masu ruwa da tsaki na Shirin LULU DA ANDALU.
Rubutawa Shariff Ahlan fassara Yaya Muhammad.