Aƙalla ƴan bindiga sama da 200 jami’an staro su ka hallaka a jihar Neja.

An far wa ƴan bindigan ne a maɓoyarsu da ke dazukan Wushishi, Mokwa, da Lavun, sai ƙaramar hukumar Mariga duka a jihar Njea.

Kwamishinan al’amuran staro a jihar Emmanuel Umar ne ya sanar da haka wanda ya ce an ƙwato dabbobi da babura da saran abubuwan amfani daga hannun ƴan bindigan.

Ya ce an jikkata wasu da dama daga ƴan bindigan da jami’an staro su ka yi arangama da su sannan wasu daga cikin jami’an tsaro sun samu rauni yayin da biyu su ka rasa rayuwarsu.

Kwamishinan tsaro a jihar ya ce fafatawar ta faru ne tsakanin ranar Lahadi zuwa ranar Talata.

Ya ce an ƴan bindigan da aka hallaka yara ne ga Bello Turji, da Kacalla sai Kawajo da Yellow Jonbros, kuma an hallaka wasu daga cikin kwamandojin ƴan bindiga a jihar.

Yayin da mu ka zanta da guda mazauna garuruwan da aka kai musu hari a ƙaramar hukumar Kontogara, Abubakar ya shaida cewar ƴan bindigan sun sace shanunsa da na ƙaninsa fiye da 60 yayin da su ka kai wani hari.

Ya ce ƴan bindigan sun tare makiyayansu a ranar Asabar sannan su ka kwashe dabbobinsa da na kaninsa.

Ya kara da cewa akwai shanu takwas da su ka dawo daga cikin waɗanda ƴan bindigan su ka sace.

A ƙarshen makon da ya gabata ma sai da yan bindiga su ka shiga wasu ƙauyuka a ƙaramar hukumar Lavun tare da sace wasu amare bayan sun ƙaddamar da wasu hare-hare a ranarkun Asabar da Lahadi.

Leave a Reply

%d bloggers like this: