Akalla mutane bakwai ne au ka rasa rayukansu ciki har da wata karamar yarinya a wani hatsarin mota da ya faru a jihar Neja.

Al’amarin ya faru ranar Litinin da misalin karfe 7:00pm na yamma a Farin Doki da ke karamar hukumar Paikoro ta jihar.
Mai magana da yawun ƴan sandan jihar Wasiu Abiodun ne ya tabbatar da haka ya ce motar da ta yi hatsarin ta na ɗaukar mutane 18 a cikinta.

Ya kara da cewa akwai wasu mutane takwas a motar waɗanda su ka samu rauni daban-daban a jikinsu.

An garzaya da waɗanda su ka samu rauni zuwa asibiti domin kula da lafiyarsu.