Gwamnan jihar Kano Abdullahi Ganduje ya bukaci takwarorinsa gwamnoni su hada kai da jami’an tsaro domin inganta tsaro a jihohinsu.

Gwamna Ganduje ya bayyana haka a yayin da ya ke gabatar da jawabi a yayin wani taro sa aka yi a jami’ar Anambra ranar Juma’a.
Laccar da ya gabatar mai taken ” Challenges Of Security And National Building” gwamna Ganduje ya ce ya na da kyau a shigar da fasahar zamani domin inganta tsaro a Najeriya.

Sannan ya bukaci gwamnonin su samar da tsarin sake bayar da horo a kai a kai ta yadda jami’an tsaro za su kasance cikin ahiri a kowanne lokaci.

A wata sanarwa da mai babban sakataren yaɗa labaran gwamnan Kano Malam Abba Anwar ya sanyawa hannu ranar Juma’a, sanarwar ta ce, gwamna Ganduje ya ce tuni jihar Kano ta yi nisa wajen amfani da fasahar zamani da kuma ɗaukar matakin aiki kafaɗa da kafaɗa da jami’an tsaro kuma jihar ta ga amfanin haka a bayyane.
Sa’annan jihar ta sake ƙarfafa alaƙa tsakanin jami’an tsaro na sa kai, da kuma samar da kayan aiki ga jami’an tsaro domin karfafa musu gwiwa.
Kuma gwamnatin jihar na tuntubar masu ruwa da tsaki a bangaren tsaro domin ba ta shawara ta yadda jihar za ta ci gaba da zamtowa cikin zaman lafiya a kowanne lokaci.