Ahmad Sulaiman Abdullahi

Ƙungiyar malaman jami’a ASUU, na shirin tsawaita wa’adin yajin aikin da suka tafi zuwa makonni 8 sakamakon rashin cimma matsaya da gwamnati kan ɓukatunsu.

ASUU ta shiga yajin aikin ne sakamakon abin da ta bayyana a matsayin gazawar gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari wajen aiwatar da yarjejeniyar da suka kulla a baya game da yadda za a inganta harkokin karatun jami’a na ƙasar.

Farfesa Abdulkadir Muhammad Danbazau jami’i ne a ƙungiyar ta ASUU, ya ce ana tattaunawa kan matakin ƙara wa’adin ne domin bai wa gwamnati damar cimma sahihiyar matsaya, ta yadda ba sai sun ƙara tafiya wani yajin aikin nan gaba ba.

Danbazau ya ce makonni 8 sun wadatar matukar gwamnatin da gake ta ke kan ɗaukar matakin da ya dace.

ASUU dai na ganin yajin aikin ne hanyar ƙarshe da take bi domin tilasta wa gwamnatin Najeriya biya mata buƙatunta.

Tun a ranar Litinin 14 ga watan Fabarairu ne ƙungiyar malaman jami’o’i, ASUU, ta tsunduma yajin aikin gargadi ga gwamanatin tarayya na tsawon wata guda.

Yajin aikin malamai a Najeriya ya fi yin tasiri a kan ɗalibai waɗanda ke tsintar kansu cikin damuwa, dalilin da ya sa wasu ke ganin ya kamata Kungiyar ta sauya salon tunkarar rikicinta da gwamnatin ƙasar ba sai lallai ta hanyar yajin aiki ba.

Wasu bayanai sun nuna cewa Ƙungiyar ta ASUU ta daka yajin aiki sau 15 tun bayan komawar Najeriya mulkin dimokuraɗiyyar a 1999, lamarin da kan jefa harkokin karatu cikin mawuyacin hali.

Leave a Reply

%d bloggers like this: