Rahotanni daga jihar Borno na tabbatar da cewar rundunar sojin saman Najeriya ta hallaka wani babban kwamandan ƙungiyar ISWAP masu ikirarin jihadi a nahiyar Afirka ta yamma.

Sabon jirgin yaƙi na Super Tucano ne ya yi luguden wuta a maƙoyan mayaƙan ISWAP har ma su ka kashe Sani Shuwaram babban kwamandan ƙungiyar.

Jaridar PRNijeroya ta ruwaito cewar an hallaka kwamandan ƙungiyar da kuma wasu mambobin ƙungiyar yayin da jirgin ya kai hari.

Jaridar PRNijeriya ta ce ƙungiyar ISWAP ta nada Malam Baƙo a matsayin sabon shugaban ƙungiyar.

Harin dasojojin saman Najeriya su ka kai maboyar mayaƙan Boko Haram stagen ISWAP a maɓoyarsu a ke cikin wani daji a ƙaramar hukumar Marte iyaka da kasar Chadi.

Rahotanni sun tabbatar da cewar wasu manyan jagororin ƙungiyar sun rasa rayukansu a sakamakon harin da sojin saman Najeriya su ka kai musu.

Rundunar sojin Najeriya ba ta tabbatar da kashe shugaban ƙungiyar ba zuwa yanzu ta ce ta na kan ƙaddamar da hare-hare har sai ta kammala aikin da ta saka a gaba kafin fitar da bayani a kai.

Leave a Reply

%d bloggers like this: