Aƙalla mutane 75 ƴan bindiga su ka saki bayan sun kwashe fiye da watanni biyu a hannunsu.

Sakin mutanen ya biyo bayan bai wa ƴan bindigan naira miliyan huɗu tare da kafawa mutanen ƙauyukan sharruɗa .

Ƴan bindigan sun saki mutanen waɗanda aka sace a garin Yar Katsina da ke yankin Kekun Waje a ƙaramar hukumar Bunguɗu ta jihar Zamfara.

Ƴan bindiga sun sace mutanen ne a wasu hare-hare da su ka kai ƙauyukan watanni biyu d su ka gabata.

Rahotanni sun tabbatar da cewar ƴan bindigan sun fara sace mutane  61 a ƙauyukan, sannan su ka sake komawa bayan kwanaki 36 kuma su ka sace sama da mutane 10.

Sai dai yan bindigan sun riƙe wata yarinya yar shekara shida a duniya kamar yadda su ka bayyana wa iyayen yarinyar bayan sun sake su.

Tuni aka mayar da mutanen da aka saki zuwa ga yan uwansu, sai dai mahukunta basu magantu a dangane da sakin mutanen ba.

Leave a Reply

%d bloggers like this: