Yayin da ta ke ci gaba da aikin murkushe ayyukan yan bindiga a arewa maso gabashin kasar nan, rundunar sojin Najeriya ta sanar da hallaka wani babban kwamandan ISWAP a jihar Borno.

Sojojin sun bayyana cewar sun hallaka babban kwamandan ISWAP a jihar Borno a yain wani hari da su ka kai musu a jihar.

Rundunar ta ce ta kashe wasu daga cikin mayakan ISWAP a yayin da ta kai musu harin.

Rundunar sojin Najeriya ta ce ta hallaka kwamandan mai suna Abubakar Danbudama da kuma wasu ƴan ƙungiyar su 19.

Harin da aka kai wa mayakan sojojin ssun ce sun yi amfani da jiragen yaki a yayin da su ka samu nasarar kashe mayaƙan a yankin tafkin chadi.

A wasu rahotannin kuwa an tabbatar da cewar mayakan ISWAP na ci gaba da kai hare-hare tare da tilastawa wasu mutanen yankuna biyan haraji.

Leave a Reply

%d bloggers like this: