Gwamnatin jihar Gombe ta amince da ɗaukar sabbin malaman makaranta 1,000 a faɗin jihar.

Gwamnan jihar Muhammad Inuwa Yahaya ne ya amince da ɗaukar sabbin malaman makarantar kuma tuni ya bai wa hukumar kula da malaman makarantu a jihar umarni.

Matakin hakan na zuwa ne bayan da gwamnatin ta fuskanci akwai ƙarancin malaman makarantun sakandire a fadin jihar.

Sannan gwamnan ya amince da bukatar sauya wurin aiki na ma’aikata 288 zuwa ma’’aikatar ilimi ta jihar domin rarrabasu a makatun sakandire da kwaleji.

Shugaban hukumar kula da malamai a jihar Na’omi Philip ta ce gwamnatin ta damu a kan ƙarancin malaman makaranta da ake fuskanta.

Ta ce gwamnatin ta fara tsara yadda za a inganta harkar ilimi ta hanyar ɗaukar ƙwararrun malaman makaranta da su ka cancanta.

Leave a Reply

%d bloggers like this: