Mutanen sun bayyana cewar su na cikin mawuyacin hali wanda su ke roƙo gwamnati ta yi duk mai yuwuwa domin ceto su.

Aƙalla mutane 68 daga cikin fasinjojin jirgin ƙasa ne ke tsare a hannun yan bindiga a jihar Kaduna.
Wani faifen bidiyo da maharan su ka wallafa ya nuna mutane da su ka bayyana kansu da fasinjojin jirgin ƙasan waɗanda aka yi garkuwa da su a ƙarshen watan da ya gabata.

Mutanen sun bayyana cewar su na cikin wani hali tare da roko gwamnati da ta biya wa ƴan bindigan buƙatunsu domin fitar da su daga halin da su ke ciki.

Daga cikin mutanen da ke tsare a hannun ƴan bindigan akwai mata 41 da maza 22 sai ƙananan yara guda biyar.
A baya maharan sun saki babban daraktaktan bankin manoma a Najeriya wanda ya roki gwamnati da ta biya wa mutanen buƙatunsu a wani faifen bidiyo da su ka fitar.
Daga cikin mutanen da ke tsare a hannun yan bindigan waɗanda su ka yi magana har da wata da ta bayyana kanta a matsayin ma’aikaciya a hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa INEC.
A ranar 28 ga watan Maris ɗin da ya gabata ne wasu yan bindiga da ake zargin mayaƙan Boko Haram ne su ka fr wa jirgin ƙasa ta hanyar dasa bom tare da kashe wasu sannan su ka yi awon gaba da wasu.