Gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje ya bai wa masu muƙamai a gwamnatinsa da su sauka daga kujerarsu zuwa ranar Litinin.

Hakan na ƙunshe a cikin wata sanarwa da babban sakataren yaɗa labarai gwamnan Kano Malam Abba Anwar ya sanyawa hannu ranar Asabar.
Gwamnan ya ce wajibi ne mutanen da su ke son tsayawa takara kuma su ke riƙe da muƙamai a gwamnatinsa su sauka zuwa ranar Litinin.

A cewar gwamnan, sauka daga muƙaman nasu ne zai sa su yi biyayya ga sashe na 84 (12) na sabuwar dokar hukumar zaɓe.

Tuni wasu daga cikin masu riƙe da muƙamai su ka sauka daga kujerarsu a kwanakin baya.
Mutane da dama na nuna sha’awar tsayawa takara a matakai daban-daban yayin da ake tunkarar zaɓen shekarar 2023.
Dakyau