Fadar shugaban ƙasa a Najeriya ta ce matsalar rashin staro da ake fuskanta a ƙasar musaman a arewaci ta zo ƙarshe.

Mai magan da yawun shugaban ƙasa Malam Garba Shehu ne ya sanar da haka a tattaunawarsu da jaridar Nation.

Ya ce a wannan lokaci gwamnati ta ɗauki babban mataki na samar da kayan yaƙi ga jami’’an tsaro da kuma haɗa tawaga ta ƙwarararrun jami’an domin kawo karshen matsalar tsaro a Najeriya.

Ya ƙara da cewa bisa nasarorin da jami’an ke smau a kan yan bindiga a ƴan kwanakin nan na nuni da cewar ƙarshen dukkanin ayyinasu ya zo ƙarshe.

Ya ƙara da cewa a halin da ake ciki mafi yawa daga cikin ayyukan ƴan bindiga ya ragu da kaso mai rinjaye wanda hakan ke tabbatar da nasarar ayyukan gwamnatin a yanzu.

Sannan a halin da ake ciki gwamnatin ƙasar ta tashi haiƙan domin bin dukkanin hanyoyin da su ka dace na ganin an kawo ƙarshen matsalar baki ɗaya.

Sannan gwamnatin ta amince da ware dala biliyan ɗaya domin siyo wasu jiragen yaƙi daga ƙasar amuruka don magance matsalar baki ɗaya.

Leave a Reply

%d bloggers like this: