Rundunar sojin Najeriya hadin gwiwa da sauran jami;an tsaro sun samu nasarar hallaka mayaƙan ISWAP 100 tare da kwamandojinsu goma a wani yankin tafkin chad.

Mai magana da yawun rundunar staron hadin gwiwar Kanal Mumammad Dole ne ya sanar da haka a wata sanarwa da ya fitar ranar Lahadi.

Ya ce an kai wa mayaƙan harin ne ta sama da ƙasa wanda su ka samu nasarar halaka mayaƙan da yawa ciki har da kwamandojinsu.

Ya ƙara d acewa jami’an staron Najeriya da na Nijar hadin gwiwa da na ƙasar Kamaru ne su ka fafata a yayin harin da aka kai wa mayaƙan.

Ya ce harin da su ka kai wa mayaƙa ya biyo bayan wai rahoton sirri da su ka samu a kan su wanda ya kai ga samun nasarar su.

Sannan sun kuɓutar da wasu mutane da dama ciki har da mata da ƙananan yara, haka kuma sun ƙwato wsu kayan abinci da kayan may da sauran kayan amfani kuma tuni su ka lalata kayayyakin.

Leave a Reply

%d bloggers like this: