Daga Khadija Ahmad Tahir

Wasu “yan bindiga da su ka yi garkuwa da wasu mutane a karamar hukumar Chikun ta Kaduna sun hallaka mutane uku inda kuma su ka nemi kudin fansar sauran waɗanda ke hannunsu.
Mai magana da yawun rundunar “yan sandan jihar Muhammad Jalige ne ya tabbatar da kisan mutanen daga cikin waɗanda ƴan bindiga su ka yi garkuwa da su.

A makonni biyun da su ka gabata ne dai “yan bindigan su ka kai hari cikin karamar hukumar inda su ka hallaka wani mutum sannan su ka yi garkuwa da wasu dama.

Wata majiya ta bayyana cewa “yan bindigan sun kira mutanen garin a waya inda su ka bayyana wa “yan garin cewa su ne su ka dauki gawarwakin mutanen da su ka hallaka a garin dutse da ke kan hanyar Kaduna zuwa Abuja sakamakon rashin biyan su kudin fansa.
Mazauna garin sun yi kira da gwamnati da ta kai musu dauki su ceto sauran mutanen da ke hannunƴan bindigan.