Daga Khadija Ahmad Tahir

Gwamnan Jihar Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje ya amince da ajiye aikin mutane bakwai daga cikin kwamishinoni a gwamnatin sa.
Hakanna ƙunshe cikin wata sanarwa da babban sakataren yaɗa labaran gwamnan Malam Abba Anwar ya fitar a yau Talata.

Ajiye muƙaman kwamishioni bakwai ɗin na zuwa ne bayan da gwamna jihar ya bayar da umarni ga waɗanda su ke da burin tsayawa takara su sauka daga muƙamansu domin mutunta sabuwar dokar hukumar zaɓe.

Abba Anwar ya kara da cewa gwamna Ganduje ya mika godiyar sa ga kwamishinonin sakamakon gudummawar da su ka baiwa Jihar Kano.
Daga Cikin wadanda su ka sauka daga kan mukaman nasu sun hada Kwamishinan ƙananan hukumomi Murtala Sulan Garo, Kwamishinan gona Dr Nasiru Yusuf Gawuna, Ibrahim Ahmad Karaye, Dr Mukhtar Ishak Yakasai, Hon.Muhammad Muhammad Santsi, da Musa Ilyasu Kwankwaso, sai Hon Kabiru Ado Lakwaya.
Sabuwar dokar hukumar zaɓe ce ta umarci masu riƙe da muƙaman siyasa da su sauka muddin su na da burin tsayawa takara a shekarar 2023.