Connect with us

Labarai

Tsakanin Karatun Allo/Almajiranci Da Bara – Daga Abubakar Murtala Ibrahim

Published

on

Almajiranci/karatun Allo/Bara

Wallafawar Abubakar Murtala Ibrahim
(#Abbanmatashiya)
08030840149
Menene almajiranci?
Almajiranci kalma ce, aikatau, a kan laƙabawa wanda aka kai karatun allo wani gari ko wata ƙasa domin mayar da hankali wajen karantar alƙur’ani mai tsarki.
Karatun allo kuwa ya samo asali ne tun bayan da addinin musulunci ya wanzu a wasu sassan Afrika da ƙasa Najeriya musamman wasu jihohin arewaci.
Mutane na ɗaukar ƴaƴansu da su ka haifa tare da kai su wajen malami da ya karanci alƙu’ani domin ƙauna da soyayyar da su ke yi wa ƴaƴansu ta yadda za su zamto gangaran a fagen karatun addini wanda shi ne tushe.
Al’ummar arewa na ci gaba da ɗabbaga wannan al’ada domin girmama malamai na soro da kuma ƙarfafar ƴaƴansu don ganin sun kasance masu fahimtar Alƙur’ani mai tsarki.
Akwai abubuwa da dama waɗanda ke tattare a ƙarƙashin karatun allo wanda hakan ke koyar da mutane rayuwa ta dangana, dagewa, mayar da hankali da naci ba tare da nuna fifiko ba kasancewar dukkanin ɗaliban iri ɗaya ake ɗaukar su.
Mutanen da masu arziƙi ne sannan masu dukiya ne amma hakan ba ya hana ɗaukar ƴaƴansu domin kai su karatun allo wata ƙasar, ko jihar ko kuma unguwa.
Wasu daga cikin iyaye a wancen lokaci na ɗaukar kayan abinci tare da kai ziyara lokaci zuwa lokaci a makarantun da su ka kai ƴaƴansu domin nuna godiya da girmamawa sannan su san halin da ƴaƴansu ke ciki.
Kasancewar a baya akwai sauƙin al’amura musamman ɓangare abincin malaman kansu bas su damu da sai iyaye sun kawo abinci ba, domin da yawa daga cikin malaman na da gonaki waɗanda su ke nomawa sannan su ciyar da ɗaliban da ke gabansu ba tare da ƙyashi ko gajiyawa ba.
A kwana a tashi rayuwa ta fara sauyawa wanda ta kai wasu malaman sun tsinci kansu a cikin gari, babu gonakin da za su noma balle su iya ciyar da dukkan almajiran da ke gabansu wanda hakan ya sa mutanen unguwa ke iya ɗaukar masu taimaka musu daga cikin almajiran tare da ciyar da su.
Idan za a iya tunawa a baya kaɗan wato shekaru ƙalilan da su ka shuɗe za ka iske wasu almajirai na zaman siɗi musamman idan su ka ga magidanta na cin abinci bayan sallar magriba ko sallar isha’i.
Hakan ta ƙara matsewa rayuwa ta ƙara tsadar da ba a iya ɗaukar wannan ma, hakan ya sa wasu almajiran ke zuwa bara gida-gida domin samun abinci na wani lokaci a hakanma dai su na samu ko dai a gidan malamin su kuma a wani gida da su ke yin aikatau.
Baya ga wannan bara da su ke zuwa na wani lokaci domin samun abincin ko dai na rana ko na dare, a dukkanin ranakun Alhamis da Juma’a almajiran na zuwa cin kasuwa a ƙauyuka idan kuwa a cikin gari ne su na zuwa wasu kasuwani mafi kusa, a wancen lokacin ba bara su ke zuwa ba, su na yin ko dai dako, ko kuma yin wani aiki da za su sami wani abu da za su siyi sabulu don yin wanki, ko kuma wani abu kamar tawada, allo, alƙalami da sauransu.
Tsadar rayuwar da mu ke ciki a yau ta tilastawa wasu daga cikin malaman makarantun allo janye ranar Talata domin bai wa almajiransu dama don ci gaba da irin wancen aikatau domin samun kuɗin da za su cike giɓin da su ka rasa.

Mecece Bara, Kuma su waye su ke bara?

Bara wani aiki ne da mutane kan fita walau masu buƙata ta musamman, ko gajiyayyu (tsofaffi) ko kuma wasu daga cikin mutane marasa godiyar Allah.
Ko a zamanin baya shekarun da su ka gabata da wahala ka ga wasu mabarata ko dai daga ɓangaren masu buƙata ta musamman ko kuma mata da maza gajiyayyu sun yi nisan zango wajen yin ta.
Su na zuwa ranakun kasuwa, ko kuma gefen wata bishiya ko wata ƴar hanya da mutane ke zirga-zirga tare da yi wa masu tafiya addu’a ala-bashshi idan ka yi niyya ko ra’ayi ka bayar da sadaka a garesu.
A kan bai wa mutane masu buƙata ta musamman ko tsofaffi sadaka domin kwaɗayin addu’ar bakinsu.
A zamanin yau da mu ke ciki bara ta zamto tamkar sana’a, domin wasu na tasowa daga wasu ƙauyuka su taho bara, daga ciki kuwa akwai matan aure, zawarawa, da ƙananan yara maza da mata wanda wasu ɓata gari daga cikinsu ma ake lalata da su a cikin gari.
A wani bincike da na yi kwanakin baya na gano wasu mutane da suke zuwa ƙauyuka domin ɗakko yara haya da zumman kawosu birni bara, idan aka samu kuɗin ana kai wa iyayensu wani kaso daga abinda aka samu na barar.
Amma mu sani sannan mu fahimta, su irin waɗannan mutane da su ke zuwa domin yin bara, ba fa almajiranci su ke zuwa ba, sannan ba karatu su ke yi a gaban malaman allo ba, aa, barar dai su ke zuwa yi, a haka wasu idan idanunsu ya buɗe mazan sun fanɗare su fara shaye-shaye, wasu sace-sace, wasu kuma masu kishi daga ciki su dinga yin sana’ar dogaro da kai da ƴan buga-guga don rufawa kansu asiri.
Kun ga ke nan akwai bambanci tsakanin almajirin da ya ke gaban malami ya na karatun allo da kuma irin waɗancan da ake ɗakkowa haya don yin bara a cikin gari.
Har gobe akwai wannan al’ada ta malam bahaushe domin ɗaukar ƴaƴansu wajen kai su gaban malamai a wasu garuruwan domin karatun Alƙur’ani, amma sai aka sami wasu ko dai rashin sani ne ko kuma kwangila ce, sai su ke alaƙanta karatun allon da irin wannan barar da na fayyace muku domin kassara karatun da rage masa karsashi a idon duniya.

Ta yaya za a magance matsalar barar da ake cece-ku-ce a kanta?

Alhaki ne na gwamnati domin wasu jihohin na yin kamen almajirai tare da mayar da su gaban iyayensu.
To amma da ake kama almajiran, nawa ne su ke faɗar ga malamin da sju ke karatu a gabansa?
Za mu ga cewar adadin almajiran da ake kai wa ma ya ragu, amma almajiran da ke bara a cikin gari sun ninka tunanin mai lissafi.
Idan gwamnati ta so, za ta iya ɗaukar mataki na hana irin waɗancan mutane yin bara domin inganta tsaro, tarbiyya da kuma tsaftace jihohin arewa.
Akwai mutanen  a cikin garin su ke su ke zuwa ƙauyuka su na ɗakko yara ƙananan domin kawo su bara, wasu kuma a na kawo musu ne har inda su ke, to gwamnati ta bincika sai ta ga hanyar da ta fi dacewa domin kawo gyara a lamarin.
Amma ina mai tabbatar da cewar karatun Al’ƙurani daban ne, kuma ba wani abu da zai sauya daga yadda ake domin ba almajiran makaranta Alƙur’ani ne ke watangaririya a titi ba.
Idan rubutu na bai maka/miki daɗi ba don zan kashe muku kasuwar kwangila ku yi haƙuri.
Bissalam
Abubakar Murtala Ibrahim
#Abbanmatashiya
22 Ramadan 143
23 Afrilu 2022

Click to comment

Leave a Reply

Labarai

Gwamnatin Tarayya Ta Gargadi ASUU Kan Watsi Da Umarnin Kotu

Published

on

Gwamnatin Tarayya ta ja kunnen Kungiyar Malaman Jami’a akan ƙin bin dokar Kotun Ma’aikatun Kasa ta Najeriya na komawa bakin aikinta daga dogon yajin aikin da ta ke yi.

Chris Ngige, Ministan Kwadago da Ayyuka, ya ce Kungiyar tana faɗawa ‘yan Najeriya zancen da babu sui akan batun cikashe fom din daukaka karar akan umarnin kotu.

Ministan ya yi kira ga kungiyar akan ta mutunta umarnin kotun, ta kuma koma kan aikinta yayin da su ke kokarin ganin sun sasanta akan sauran matsalolin.

Ministan ya yi wannan batun ne ta wata takarda da aka fitar a ranar Lahadi wadda Olajide Oshundun, mataimakin darektan yaɗa labaran ministan ya sanyawa hannu.

A cewar sa kungiyar ba ta fadin asalin gaskiyar yadda aka yi da ita ga mutanen ƙasa da kuma mambobinta, dangane da batun daukaka kara bisa umarnin da kotu ta yi mata ranar 2 ga watan Satumba.

Sai dai ASUU ta bukaci a ba ta damar daukaka kara. Sannan ta hada wannan bukatar tata da kuma takardar daukaka karar da ta ke da niyar yi da zarar an bata wannan damar.

Continue Reading

Labarai

Jami’an NDLEA Sun Kama Mai Yin Safarar Miyagun Kwayoyi A Abuja

Published

on

Hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa NDLEA, ta cafke Misis Pamela Odin, ‘yar shekaru 32, bisa yunkurin safarar alluran Rohypnol mai nauyin kilogiram 2.150 ta filin jirgin saman Nnamdi Azikiwe da ke Abuja.

Daraktan yaɗa labarai na hukumar NDLEA Femi Babafemi ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a jiya Lahadi a Abuja.

Babafemi ya ce an kama matar ne a ranar 23 ga watan Satumba, yayin da take yunkurin shiga jirgin sama kamfanin jirgin saman Turkiyya dauke da maganin a boye a cikin barkono da kuma wasu cushe a cikin kayan abinci.

Ya ce wacce ake zargin ‘yar asalin kauyen Afiesere ne a karamar hukumar Ughelli ta Arewa a Delta, ta yi ikirarin cewa tana gudanar da wani gidan cin abinci a birnin Istanbul na kasar Turkiyya.

Babafemi ya kara da cewa ta yi ikirarin cewa ta zo Nijeriya ne domin ganin ƴan uwanta da kuma siyan kayan abinci don kasuwancinta na gidan abinci ƙasar.

Continue Reading

Labarai

Wani Matashi Ya Hallaka Ƙaninsa Lokacin Da Ya Ke Gwada Maganin Bindiga A Kansa

Published

on

Wani matashi ya harbe kaninsa mai shekaru 12 yayin gwada maganin bindiga a Karamar Hukumar Kaima ta Jihar Kwara.

Wadandan lamarin ya shafa dai ’ya’yan wani mafarauci ne da suka mallaki wani sabon maganin bindiga kuma suka yi yunkurin tabbatar da ingancinsa.

A cewar manema labarai lamarin ya faru ne a ranar Lahadi, inda wanda ya yi aika-aikar tuni ya arce ya bazama cikin daji bayan mai aukuwar ta auku.

Da yake zantawa da manema labarai a yau Litinin, jami’in hulda da al’umma na rundunar ’yan sandan jihar, Okasanmi Ajayi, ya ce Kwamishina ’Yan sanda Paul Odama ya bayar da umarnin a fara bincike a kan lamarin.

Okasanmi ya ce bayan sun daura maganin bindigar a jikinsu, sai babban cikinsu ya yi amfani da bindigar mahaifinsu ta farauta ya harbi kaninsa.

Sai dai an yi rashin sa’a maganin bai yi aiki ba, lamarin da ya sanya nan take kanin da aka harba ya mutu.

Okasanmi ya shawarci iyaye da subrika zuba idanu kan duk wani motsi na ’ya’yansu domin gudun faruwar mummunan lamari makamancin wannan.

Continue Reading

Talla

Trending

%d bloggers like this: