Hukumar kashe gobara a jihar Kano ta samu nasarar ceto wani zakara da ya faɗa rijiya.

Hukumar ta samu kiran waya daga wani a unguwar Ƙwalli kusa da makarantar S.A.S sannan aka sanar musu da faɗawar zakaran.
Bayan samun rahoton hakan su ka tashi dakarunsu uwa wajen kuma sun samu nasarar cetoshi a raye.

Mai magana da yawun hukumar Saminu Yusif ya ce an ceto zakaran mai shekara guda kuma an mika shi ga masu shi.
