Hukumar tsaron farin kaya a Najeriya DSS ta yi kira ga ‘yan Najeriya da su kula sosai gabanin gabatowar bukuwan karamar sallah sakamakon wani yunkuri da ta gano wasu ‘yan ta’adda na shirin yi a lokacin bikin sallar.
Hukumar ta ce ‘yan ta’addan na yunkurin kai hare-haren a gurare daban-daban na fadin Najeriya ciki harda guraren yin ibada.
Mai magana da yawun hukumar Peter Afunnanya shine wanda ya sanar da hakan a yau Talata a cikin wata sanarwa da ya fitar.
Peter ya ce dukkan wasu gurare da mutane ke taruwa ya kama a sanya matakan tsaro a gurin domin gujewa yunkurin na ‘yan ta’addar.
Kakakin ya bayyana cewa ‘yan ta’addan na son mayar da kasar kamar lokacin da ake saka boma-bomai a wasu guraran.
Peter ya kara da cewa hukumar su ta shirya tsaf wajen ganin sun hada gwiwa da sauran hukumomin tsaro domin ganin an dakile duk wani yunkuri na bata gari don ganin mutanen sun samu nutsuwa a duk inda su ke.
Hukumar ta kuma yi kira ga al’umma da su cigaba da yin mu’amalar su kamar yadda su ka saba.

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: