Mutane da dama ne su ka jikkata yayin da guda ya rasa ransa a lokacin da aka yi arangama tsakanin mabiya mazahabar shi’a da jami’an tsaro.

Mabiya shi’a sun fita zanga-zanga da su ka fara ranar Juma’a a matsayin ranar ƙudus da nufin nunawa duniya ƙin amincewa da muzgunawar da ake yi wa falasɗinawa.

Mabiya shi’a sun tafi a kan babbar hanyar Kaduna zuwa Zaria sai dai jami’an tsaro sun yi koƙarin dakatar da su lamarin da ya koma rikici.

Wani da lamarin ya faru a kan idonsa ya shaida cewar jami’an tsaro sun yi amfani da harsashi mai kis da kuma hayaƙi mai saka hawaye, yayin da mabiya shi’a su ka ƙone wasu ababen hawa a Zaria.

Shugaban mazahabar shia a Kaduna Aliyu Umar a shaidawa jaridar Daily Trust cewarzanga-zangar da ake yi a kan masallacin ƙudis duk shekara ana yi ne a kowacce kasa a faɗin duniya.

Shugaban y ace sun fara gudanar da zanga-zangar tasu cikin lumana sai dai jami’a tsaro sun ɓata tsarin daga bisani.

Ya kara da cewa a halin da ake ciki akwai mabiyansu mutane takwas da jami’an staro su ka kama a yayin zanga-zangar.

Rundunar yan sanda a jihar ba ta ce komai a dangane da lamarin ba har lokacin da mu ke kammala labarin.

Leave a Reply

%d bloggers like this: