Ahmad Sulaiman Abdullahi

 

 

An gurfanar da Fasto Abraham malamin addini a kotu wanda ya faɗa ma mabiyansa cewa yana iya kai su aljannah, inda yace  musu Omuo-Ekiti ne ƙofar shiga aljanna.

Fasto Abraham dai ya nemi mabiyansa su biya kuɗi N310,000 domin shiga aljannah bayan ya ce masu ya san hanyar da ake bi a shige ta.

An gurfanar da faston a wata kotun majistare ta jihar Ekiti da ke zama a Ado-Ekiti.

Ɗan sanda mai gabatar da ƙara, Sufeto Johnson Okunade, ya ce laifin ya saɓa wa sashe na 416 na dokar laifuka ta jihar Ekiti na shekarar 2012.

Johnson ya ƙara da cewa kai Fasto Noah Abraham Adelegan a ranar 27 ga watan Afrilu, a Omuo Oke-Ekiti a yankin Omuo, ta hanyar karya da niyar zamba, ka gabatar da kanka ga taron jama’a a cocin Christ High Commission Ministry, Omuo, Oke-Ekiti, a matsayin wanda zai iya kaisu aljannah kafin tashin duniya.

Inda nan take suka biya kuɗi daga N300,000 zuwa N310,000 kwannensu.”

Lauyan wanda ake ƙara, Adunni Olanipekun, ya buƙaci kotun da ta bayar da belin wanda yake karewa, inda ya ƙara da cewa a shirye yake ya gabatar da amintattun wadanda za su tsaya masa.

Sufeto Okunade yace bashi da ja akan buƙatar belin, amma ya buƙaci kotun da ta yi amfani da damar ta wajen bayar da belin ko kuma ƙin amincewa da shi.

Alkalin kotun mai shari’a Titilola Olaolorun ta bayar da belin wanda ake ƙara a kan kudi N100,000 tare da mutane biyu da za su tsaya masa.

A ƙarshe mai shari’ar ta ɗage sauraron karar zuwa ranar 24 ga watan Mayu.

Leave a Reply

%d bloggers like this: