Labarai
Mutane Biyar Sun Rasa Rayukan Su Sakamakon Ruwan Sama A Damaturu
Kimanin mutum biyar ne suka rasa rayukansu yayin da mutane da yawa suka jikkata bayan saukar wani mamakon ruwan sama mai tafe da kakkarfar iska da guguwa a Damaturu, babban birnin Jihar Yobe.
Jaridar Daily Nigerian ta ruwaito Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta jihar SEMA ta tabbatar da afkuwar lamarin inda ta ce fiye da gidaje 100 ne suka lalace sakamakon iftila’in.
Sakataren SEMA na jihar, Mohammed Goje ya ce sun samu labarin lamarin ne daga wasu mutane a ranar Litinin 9 ga watan Mayun 2022, wadanda suka taimaka wajen gaggawar kai wadanda suka jikkata zuwa asibiti.
Mohammed Goje ya kuma tabbatar da cewa mutum biyar sun riga mu gidan gaskiya daga cikin 41 da lamarin ya rutsa da su, kuma mutanen sun fito ne daga yankuna daban-daban a birnin na Damaturu, inda aka wuce da su asibiti.
Yankunan da abin ya shafa sun hada da Waziri Ibrahim Extension da Abbari Extension da NayiNawa da Pompomari da rukunin gidajen ‘yan Majalisar Dokokin jiha da Gujba Road da kuma Maisandari.
Labarai
An Bai Wa Kamfanin Wutar Lantarki Mako Guda Ya Cire Karin Kudin Wutar
Ƙungiyar ƴan kasuwa a Najeriya ta bai wa hukumar samar da wuta a Najeriya mako guda da ta janye batun ƙarin wutar lantarki da ta yi.
Shugaban ƙungiyar Fetus Osifo ne ya bayyana haka yau Laraba wanda ya ce sam ƙarin bai dace da ƴan Najeriya ba a wannan lokaci.
Yayin da yake jawabi a yau da ake ranar ma’aikata ta duniya, Fetus Osifo ya buƙaci a mayar da tsohon farashin wutar maimakon karin kusan kashi 300 da aka yi a kwanan nan.
Gwamnatin ta ƙara farashin ne zuwa sama da naira 250 kan kowanne megawatt guda maimakon naira 66 da ake biya a baya.
Rukunin da ke kan tsarin band A ne aka yi wa ƙarin wanda gwamnatin ta ce su na samun wuta tsawon awanni 24 a kowacce rana.
Sai dai maganar ta ci karo da wata magana da ministan makamshi ya yi cewar, ba za a taba samun tsayayyar wuta a Najeriya ba har sai an kashe dala biliyna goma duk shekara tsawon shekara goma.
Haka ma mataimakin shugaban ƙasa Sanata Kashim Shettima ya ce ƙasa da kashi 20 na ƴan kasar ne ke morar lantarki yayi da fiye da rabin ƴan kasar ba sa ta’ammali da ita baki daya.
Labarai
Dalibai Biyu Sun Rasa Ransu Bayan Shigar Su Dam Din Danbatta
Wasu ɗalibai guda biyu sun rasa ransu a yayin da su ka shiga dam din Danbatta a Kano.
Hukumar kashe gobara a Kano ta tabbatar da mutuwar ɗaliban biyu wanɗanda dukkansu ƴan kasa da shekara 25 ne.
Mai magana da yawun hukumar Saminu Yusif ya ce sun samu kiran waya ne daga wani Kwamared Ibrahim Umar Muhammad wand aya sanar da su cewar ɗaliban uku sun shiga dam ɗin Thomas kuma sun kasa fitowa.
Bayan samar da su jami’an hukumar da ke karamar hukumar Dambatta haɗin gwiwa da masunta su ka yi kokarin ceto mutum guda.
Yayin da biyun aka cetosu da yamma kuma a mace.
Daliban na karatun a kwalejin noma da kiwo da ke Danbatta, kuma tuni aka kai guda dake rage asibiti domin kula da lafiyarsa.
Lamarin ya faru a jiya Talata kamar yadda hukumar ta sanar.
Zuwa yanzu hukumar ta ce ta na ci gaba da bincike domin gano dalilin mutuwar tasu.
Labarai
NLC Ta Yi Watsi Da Batun Karin Albashi Da Gwamnatin Tarayya Ta Yi
Ƙungiyar kwadago a Najeriya ta yi watsi da batun ƙarin albashin da gwamnatin tarayya ta yi na wasu rukuni shida.
Kungiyar ta yi watsi da ƙarin tare da jaddada matsayarsu kan mafi karancin albashi naira 615,000.
A wata tattaunawa da mataimakin babban sakataren Christ Onyeka ya bayyanawa jaridar Daily Trust cewar batun bata lokaci ne kawai.
Sai dai har zuwa daren jiya da gwamnatin ta sanar da ƙarin kungiyar ba ta bayyana gamsuwa a kai ba.
Gwamnatin ta ce ta ƙarawa ma’aikatan albashin ne da kashi 25, da kuma kashi 35 ga wasu rukuni shida na ma’aikatan.
Tun tuni ƙungiyoyin kwadago ke kiraye-kiraye da a ƙara musu albashi ganin yadda cire tallafin man fetur ya taɓa al’amura da dama.
-
Labarai3 months ago
Mafi Karancin Sadaki A Najeriya Ya Koma Dubu 99,241
-
Mu shaƙata1 year ago
Kun San Ma’anar Kalmar Chiza Dani? Waƙar Da Ke Tashe A Kwanakin Nan?
-
Labaran ƙetare5 years ago
Wajibi ne duk wani namiji ya Auri mata Biyar ko a ɗaure shi a gidan yari— Sarkin Swaziland
-
Al'ada5 years ago
Fahimta ta a kan matsalar aure a ƙasar Hausa
-
Labarai5 years ago
Ba kwaya ƴan sandan kano suka kama ba, babu sinadarin maye a cikin maganin – NAFDAC
-
Addini4 years ago
Lokutan da ake saurin karɓar addu’a
-
Lafiya5 years ago
Menene Genotype ? Amfanin yinsa kafin Aure – Mujallar Matashiya
-
Mata adon gari5 years ago
Sinadarin gyaran gashi – Adon Gari