Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya roki kungiyar malaman jami’o’i (ASUU) da ta janye yajin aikin da take yi domin biyan bukatun dalibai.

Shugaban ya yi wannan roko ne a yau Alhamis a wajen bikin ranar samar da albarkatu na kasa karo na 19 da kuma bayar da lambar yabo ta National Productivity Order of Merit Award (NPOM) ga wasu fitattun ‘yan Najeriya da kungiyoyi 48 a bangarorin gwamnati da masu zaman kansu, saboda dimbin ayyukan da suke yi, da kwazo.

Buhari wanda ya bukaci ASUU da ta yi la’akari da halin da daliban ke ciki, ya kuma bukaci daliban da ke manyan makarantun gwamnati da su yi hakuri.

Shugaban kasar a wata sanarwa da mai magana da yawun sa Femi Adesina ya fitar, ya tuna cewa tun da farko ya umarci shugaban ma’aikatan fadar gwamnatin tarayya Hon. Ministocin Kwadago da Aiki da Ilimi da Kasafin Kudi da Tsare-Tsare na Kasa da su gaggauta gabatar da dukkan bangarorin kan teburin tattaunawa don sake duba bakin zaren da kungiyar ASUU ke bukata da ma sauran kungiyoyin kwadago da ke Jami’a.

Buhari, yayin da yake magana kan taken bikin na bana ‘’Samar da Ilimi Mai Kyau ta hanyar Inganta Ilimi’’, ya yi alkawarin cewa Gwamnatin Tarayya za ta ci gaba da yin duk mai yiwuwa don daukaka tsarin ilimi a kasar nan.

Ya ce gwamnatinsa ta san cewa makomar kowace al’umma ta dogara ne kan tsarin tsarin karatun ta.

Leave a Reply

%d bloggers like this: