Hukumar zaɓe mai zaman kanta a Njaeriya INEC ta ce za ta dakatar da yin rijistar katin zaɓe daga ranar 30 ga watan Yunin shekarar da muke ciki.

Shugaban hukumar a Najeriya Farfesa Mahmood Yakubu ne ya sanar da haka a ofishin hukumar da ke Abuja yayin ganawa da masu ruwa da tsaki.

Ya ce a halin da ake ciki ana ci gaba da rukunin ƙarshe na tsarin yin riistar katin zaɓe kuma za a kammala a ranar 30 ga watan Yuni.

Haka kuma hukumar za ta rufe yin rijistar katin zaɓe a yanar gizo daga ranar 30 ga watan Mayun da mu ke ciki.

Shugaban ya ce waɗanda su ka aika da bayanansu a yanar gizo, na iya zuwa domin ofishin hukumar na ƙanana hukumomi domin ɗaukar hoton fuskarsu da yatsunsu.

Hukumar ta lura cewar akwai wasu da dama da su ke maimaita rijistar sau biyu wanda hukumar ta ce hakan ya saɓa da ƙa’idar aikin.

Ko a baya sai da hukumar ta bayyana a wani taro da INEC ta shirya a Kano cewar, akwai fiye da kaso 30 na mutanen da su ka yi rijistar la’hali su na da ita a baya.

Hukumar ta ce ana yin rijistar ne ga mutanen da basu da ita kuma shekarunsu ya kai 18, ko masu matsala domin a gayar musu.

Leave a Reply

%d bloggers like this: