Gwamnatin tarayyar Najeriya ta ayyana jihohi sama da 30 da ka iya fuskantar ambaliyar ruwa a bana.

Daga cikin jihohin da su ka haɗa da kudu da arewacin ƙasar har da babban birin tarayya Abuja.

Ministan samar da ruwan sha Sulaiman Adamu ne ya bayyana haka ya ce jihohin da su ke cikin hatsarin ambaliyar ruwan akwai Legas, Kaduna, Gombe, Edo, Delta, Akwa Ibom, Abia da jihar Rivers.

Sannan akwai jihohin Bayelsa, Ogun, Imo, da jihar Cros River.

Ministan ya ce ambaliyar ruwan na iya faruwa a tsakanin watan Yuni zuwa watan Disamban shekarar da mu ke ciki.

Akwai ƙananan hukumomi 57 a faɗin ƙasar da ka iya fuskantar mummunan ambaiyar ruwan saman a tsakanin watan Afrilu zuwa watan Yuni.

Sai kuma wasu ƙananan hukumomi 220 da za su fuskanci matsalar tsakanin watan Yuli zuwa Disamba.

Minsitan ya ce jihohin da za su fi fuskantar matslaar akwai Legas, Delta,  Edo, Akwa Ibom, Abia, da babban birin tarayya Abuja.

Leave a Reply

%d bloggers like this: