Malam Abduljabbar Kabara ya ce ya kori lauyoyinsa saboda sun saɓa yarjejeniyar da suka yi.

Malamin ya bayyanawa kotun haka a yau Alhamis yayin da ake ci gaba da sauraron shari’ar.

A cewar malamin yanzu yana sake neman wasu lauyoyin da zasu tsaya masa.

Wannan shine karo na uku, da Malamin dake tsare a gidan gyara hali, ya sake watsi da Lauyoyinsa.

Malam Abduljabbar kamar yadda ya yiwa Lauyoyinsa na baya, yana zarginsu da gaza kare shi a gaban Kotu.

Su kuwa lauyoyin gwamnatin jihar Kano sun buƙaci kotun ta umurci hukumar dake baiwa marasa ƙarfi kariya a kotu kyauta, watau Legal Aid Council da ta bawa Malamin lauyan.

A ƙarshe, kotun ta amince da hakan kuma ta yi umarni ga Legal Aid Council ta bawa Abduljabar Lauyoyin da za su kare shi.

Sai dai, Malam AbdulJabbar ya buƙaci kotu ta rabu da shi zai iya cigaba da kare kansa, tunda duk lauyan da ya ɗauka sai ya ce ana yi masa barazana da rayuwarsa.

A ƙarshe mai shari’a ya ɗage zaman zuwa ranar 26 ga Mayu, 2022.

Leave a Reply

%d bloggers like this: