Shugaban kasa muhammad Buhari ya yi Allah wadai da kisan daliba a kwalejin Shehu Shagari da ke Jihar Sokoro da “yan uwan ta dalibai su ka yi sakamakon batanci ga Annabi da ta yi.

Shugaban ya bayyana cewa doka ba ta bayar da dama idan wani abu ya faru mutane su dauki doka a hannun.
A jawabin na shugaba Buhari ya bukaci a zurfafa bincike don gano wadanda su ka aikata lamarin.

Shugaban ya bayyana cewa hukumomi su ne wadanda ya kama su zartar da hukunci idan wani abu ya faru ba mutane ne za su dauki hukunci da kan su ba.

Shugaban ya kuma bayar da umarni ga hukumomi a Jihar ciki harda kamfanonin sadarwa da su aiki domin ganin an dakile dukkan wasu bayanai da ba su da ce ba da ake turawa ta kafafan sada zumunta.
A sakon na shugaba Buhari ya jajantawa iyayen dalibar sakamakon faruwar lamarin