A daren jiya Asabar wasu ƴan bindiga su ka kai hari garin ƙarfi da ke yankin ƙaramar hukumar Takai a Jihar Kano inda suka kashe mutane 6, suka raunata 2 sannan suka tafi da Sarkin garin.

Wani mazaunin garin ya shaidawa manema labarai yadda lamarin ya faru.

A cewar sa

”Wajen 12 saura na dare ƴan bindiga sun shigo garin Ƙarfi da ke ƙaramar hukumar Takai suna harbe-harbe.

Mutane ma sun ɗauka masu babura ne suke wasa, sai ganin su akai akan babura sun zo gidan Sarkin Ƙarfi suka ɗauke shi suka tafi dashi.”

Ya ƙara da cewa ƴan bindigar sun shigo ne daga ɓangaren kudancin garin inda sukai iyaka da jihar Bauchi, sun harbi mutane 8 a hanyar komawar su bayan sun yi garkuwa da Sarkin.

“Shida daga cikin waɗanda aka harba sun riga mu gidan gaskiya, yayin da ragowar mutum 2 suke kwance asibiti.

A halin yanzu anyi Jana’izar mutane 6 waɗanda suka rasu a garin na karfi”.

Munyi Ƙoƙarin tuntubar kakakin rundunar ƴan sandan jihar Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa akan wannan al’amari sai dai ba mu same shi a waya ba.

Leave a Reply

%d bloggers like this: