Jam’iyya mai mulki (APC) All Progressives Congress ta tara makudan kuɗi sama da naira biliyan 29 daga siyar da fom ɗin takarar kujeru daban-daban a babban zaben 2023.

Jam’iyyar ta (APC) ta tsawwala fom dinta na takarar shugaban ƙasa zuwa naira miliyan 100, na gwamna naira miliyan 50, na sanata naira miliyan 20 sannan na ƴan majalisar wakilai naira miliyan 10.
Babban sakataren tsare-tsare na jam’iyyar ta ƙasa, Sulaiman Argungu, ya bayyana wa manema labarai hakan a Abuja.

Ya bayyana cewa ƴan takara 145 ne suka siyi tikitin takarar gwamna, 352 suka siya don takarar zaɓen fidda yan takarar sanata.

Ya ƙara da cewa 1,197 sun yanki fom ɗin majalisar wakilai yayin da masu neman takarar shugaban ƙasa 28 ma suka yanki nasu fom ɗin.
Jam’iyyar ta tara naira miliyan 2.8 daga siyar da fom ga ƴan takara 28, naira miliyan 7.2 daga ƴan takarar gwamna 145, naira miliyan 7 daga masu neman takarar sanata.
Sai kuma naira miliyan 11.9 daga masu neman kujerar majalisar wakiali, inda jimlar kuɗin ya kai sama da naira biliyan 29.
Zuwa yanzu, muna da masu neman takarar gwamna 145. Mun kafa kwamitoci uku domin tantance su.
Muna da masu takara 351 da suka yanki tikitin takarar sanata, yayin da muke da masu neman takarar kujerar majalisar wakilai 1,197, da kwamitoci 20.
Zuwa yanzu muna da masu takarar shugaban ƙasa 28.
Kwamitocin majalisar dattawa za su kasance huɗu.
Bugu da kari, muna da tsare-tsaren jam’iyyarmu da za a baiwa kowani kwamiti don tantancewar, da kuma kwamitin ɗaukaka kara.
Muna kuma da tsari, na fom ɗin tantancewa da za a baiwa kowani kwamiti.”
Ya kuma bayyana ranar 23 ga watan Mayu a matsayin ranar tantance ƴan takarar shugaban ƙasa.