Gwamnan jihar Sokoto Aminu Waziri Tambuwal ya sassauta dokar ta ɓaci ta ɓaci da aka sanya a jihar biyo bayan zanga-zanga a kisan kisan wata da t yi ɓatanci ga annabi Muhammad S.A.W.

 

Kwamishinan yada labarai a jihar Isah Galadanci ne ya sanar da haka yau Litinin bayan samun bayanai daga hukumomin tsaron jihar.

 

Wasu matasa a jihar Sokoto sun hallaka dalibar mai suna Deborah bayan yin kalaman ɓatanci ga Annabi Muhammad S.A.W.

 

Jami’an ƴan sanda sun kama wasu matasa biyu da ake zargi da hannu an kisan dalibar.

 

Bayan kama mutane biyu a jihar wasu matasa su ka fara zanga-zanga a jihar lamarin da ya sanya gwamnatin ta saka dokar ta baci a jihar.

 

Tuni jami’an ƴan sanda su ka girfanar da mutane biyu a gaban kotu bayan zarginsu da ake da hannu wajen kisan dalibar.

 

Bayan gurfanar da matasan biyu a gaban kotu lauyoyi 34 sun tsaya domin kare waɗanda ake zargi da kashe dalibar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: