Wani jami’in gidan yari ɗauke da bindiga da ke aiki da gidan yarin Goron Dutse a jihar Kano ya harbe wani dan kasuwa mai saida sigari har lahira bayan musayar yawu da ta kaure a tsakanin su.

Jami’in gidan yarin mai suna Adamu, ana zargin ya harbe ɗan kasuwar ne bayan wata takadama tsakaninsa da ɗan kasuwan kan taba sigari.
A cewar wani ganau, ya shaida cewa Adamu ya tunkari ɗan kasuwar ne da N200 domin ya siyan taba sigari kan naira 10 kowanne.

A cewarsa:

“Ɗan kasuwan ya ƙi sayar da sigarin ga jami’in gidan yarin, nan da nan ya harbe shi sau biyu a ciki.”
Majiyar Ya ƙara da cewar, jami’in ya kuma harbi wani mutum da ke wucewa wurin a kan keke.
Yace Adamu ya kwankwaɗi miyagun kwayoyi lokacin da ya isa wurin.
Hakazalika, wasu shaidu sun bayyana cewa, alamu sun nuna ɗan kasuwan na bin jami’in bashi ne, wanda ya hana shi ninka bashin har ta kai su ga cacar baki.