Wasu da ake zargi “yan bindiga ne sun aike da wata takarda wasu kananan hukumomi Tara na Jihar Anambura.

Wasikar ta “yan ta’addan na nuni da cewa za su kai hari kananan hukumomin nan bada jimawa ba.

“Yan bindigan sun aike da wasikar dukkan kananan hukumomin da su ka ayyana za su kai wa harin.

Kananan hukumomin da su ka ambata sun hada da Anambura ta gabas, Nnewi ta kudu, Awka ta Arewa, da Awka ta Kudu, Ihiala Aguata Idemili ta Arewa da Idemili ta Arewa Orunba ta Kudu da kuma Orunba ta Arewa .

Sannan a cikin wasikar ta mayakan sun bayyana wa jami’an tsaro cewa su shirya yadda za su yi musayar wuta da su.

“Yan bindigan sun kara da cewa matukar ba a sako musu shugaban su Nmandi Kanu ba to babu shakka ba za su fasa aiwatar da kudurin su ba.

Leave a Reply

%d bloggers like this: