Kwamishinan Labarai, Malam Muhammad Garba, ya yi ƙarin haske kan abinda ya fashewar daya auku

Ya ce fashewar ya faru ne a wani wurin ajiye abincin dabobbi inda ke kallon makarantar a Aba Road, Sabon Gari, karamar hukumar Fagge.
Ya bayyana hakan a ranar Talata inda ya ƙara da cewa ba a makaranta ne fashewar tulun gas ya faru a Sabon Garin Kano ba.

Wasu na fargabar cewa ƴan ta’adda sun fara kai hari makarantu a Kano bayan abin da ya faru a kusa da makarantar Winners Kid Academy.

Garba ya bayyana cewa:
“Kawo yanzu ba a tantance dalilin fashewar abin da kuma ɓarnan da ya yi ba a hukumance.
Tuni hukuma ta fara bincike kuma za a ɗauki matakai.
“Muna kira ga mutanen jihar, musamman waɗanda ke zaune a unguwar, su kwantar da hankulansu yayin da gwamnati da hukumomin da abin ya shafa ke aiki kan lamarin.”
Kwamishinan ya bada tabbacin cewa gwamnati za ta cigaba da yi wa al’umma bayani kan cigaban da ake samu ya kuma gargadi mutane su guji yaɗa labaran da ba a tabbatar ba.
Zaku iya shiga shafin mujallar matashiya facebook/YouTube domin ganewa idanku abinda ya faru kai tsaye, kada ku bari komai ya wuce ku.