Ministan watsa labarai da al’adu na ƙasa Alhaji Lai Mohammed ya buƙaci shafin Facebook da sauran shafukan sada zumunta da su daina barin ƴan ƙungiyar IPOB da ke fafutikar kafa ƙasar Biafra su rinƙa amfani da shafin wurin neman tayar da zaune tsaye ko kuma haɗa rikicin ƙabilanci.

Ministan ya bayyana haka ne a Abuja a ranar Talata bayan wata tattaunawa da ya yi tare da wakilan kamfanin Facebook.

Lai Mohammed ya bayyana cewa tun da gwamnatin tarayya ta ayyana IPOB a matsayin ƴan ta’adda, Facebook ba shi da hurumin ba ƴan IPOB damar bayyana ra’ayinsu.

Ministan ya bayyana cewa duk da an daɗe ana ta ƙorafi ga Facebook kan ayyukan ƴan IPOB, amma kamfanin bai yi komai ba da zai dakatar da su.

Ya ce a yanzu gwamnatin Najeriya za ta ci gaba da sa ido kan Facebok da sauran shafukan sada zumunta a ƴan kwanakin nan domin tabbatar da cewa sun bi ƙa’idoji.

Leave a Reply

%d bloggers like this: