Wata babbar kotun tarayya da ke zamanta a Abuja, a ranar Laraba, ta ƙi bayar da belin shugaban ƙungiyar masu fafutukar kafa ƙasar Biafra (IPOB), Nnamdi Kanu, har sai an yanke hukunci kan laifin cin amanar ƙasa da gwamnatin tarayya ta maka shi a kotu a kai.

Mai shari’a Binta Nyako ta ce dole ne Kanu ya bayyana dalilin da ya sa ya ci zarafin belin da aka ba shi a baya, kafin ya samu wani sassaucin beli daga kotun.
A cewar mai shari’a Nyako:

“Har sai an tabbatar da batun rashin halartar wanda ake ƙara domin shari’ar da ake yi masa, tare da duk sharuɗɗan belin da aka saba, buƙatar belin a nan take zai zama ya yi sauri, don haka kotu ta hana belin.

“Duk da haka, wanda ake tuhuma yana da ƴancin sake shigar da buƙatar belin.”
Kotun ta yi nuni da cewa, shari’ar Kanu ta samu koma baya ne tun a 2015, sakamakon wasu ƙararraki 19 da aka shigar a kan batun.
Don haka, ta roƙi bangarorin da su ba da damar a ci gaba da shari’ar don a iya tantance laifin, ko saɓanin haka.
A buƙatar belin da ya shigar, Kanu, ya shaidawa kotun cewa an gana masa azaba mai tsanani na tsawon kwanaki takwas a ƙasar Kenya, kafin daga bisani a kawo shi gida Najeriya domin ci gaba da shari’arsa.
Ya yi zargin cewa yanayin lafiyarsa ya taɓarɓare, biyo bayan “wani abu mai guba” da ya ce an yi masa allurarsa, wanda ya ce yana sa shi ciwon ciki da kuma bugun zuciya.
Da yake nanata cewa hukumar ta DSS ba ta da wuraren da suka dace da duba lafiyarsa, Kanu ya shaida wa kotun cewa an tsare shi ne shi kaɗai inda ya yi zargin cewa a kullum yana gab da shiga tabin hankali.
Shugaban na IPOB ya shaida wa kotun cewa yana da “amintattun tsayayya”, da suka yi alkawarin cewa ba zai aikata wani laifi ba yayin da yake kan beli.
Baya ga haka, Kanu, ya ce babu wata kotun ƙasar da ta yi masa shari’a ko kuma ta yanke masa hukunci, yana mai cewa yana da damar a bayar da belinsa.
Ya kuma ja hankalin kotun cewa a baya an sake shi ne bisa dalilin rashin lafiya.
Sai dai gwamnati, ta buƙaci kotun da ta ƙi amincewa da neman belin, inda ta dage cewa Kanu, da ya fahimci girman ƙarar, zai gudu ne daga ƙasar, kuma ba zai miƙa kansa gaban kotu ba.