Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya tafi haɗaɗɗiyar daular Larabawa domin ganawa da sabon shugaban ƙasar ya Alhamis.

A wata sanarwa da Malam Garba Shehu ya fitar, wanda ke magana a madadin shugaban, ya ca eshugaba Buhari ya sami rakiyar ministan harkokin ƙasashen waje, ministan Abuja, da ministan sufurin jiragen sama da ministan sadarwa a Najeriya.
Sauran ƴan rakiyar tasa sun haɗa da mai bashi shawara a ka harkokin tsaro, da shugaban hukumar leƙen asiri ta ƙasa a Najeriya.

Maƙasudin ziyarar shugaban domin ta’aziyyar tsohon shugaban ƙasar tare da ganawa da sabon shugaba ƙasar Mohammad Bin Zayed Al Nahyan.

Sannan shugaba Buhari zai taya murna ga sabon shugaban ƙasar a bisa damar da ya samu.
Sannan shugaba Buhari zai sake ƙulla alaƙa mai ƙarfi tsakanin Najeriya da haɗaɗɗiyar daular larabawa, kuma ana sa ra zai dawo Najeriya a ranar Asabar.